Shugaban bangaren 'yan sandan jihar Punjab Mushtaq Ahmad Sukhera ya bayyana cewa, an kai harin a birnin Lahore, wanda yana kusa da birnin Wagah dake a iyakar kasa a tsakanin Indiya da Pakistan. Yayin da lamarin ya faru, mutane fiye da 200 sun gama kallon bikin saukar da tuta sun kama hanyar komawa gida, wani mutum ya tada bam din da ya hada da jikinsa, wanda ya haddasa mutuwa da raunatar mutane da dama, tare da lalata dakunan cin abinci da motoci dake kewayen wurin.
Bangaren asibiti ya bayyana cewa, mutanen da suka mutu a sakamakon harin sun hada da jami'an tsaro 3, da kananan yara 7 da kuma mata 11. wadansu mutane a kalla 20 sun ji rauni mai tsanani a sakamakon harin, don haka mai yiyuwa ne yawan mutanen da suka mutu a sakamakon harin zai karu.
Bayan faruwar lamarin, kungiyoyin dakaru 3 sun sanar da daukar alhakin tada wannan hari, ciki har da reshen kungiyar Taliban da ke kasar Pakistan.
Shugaban kasar Pakistan Zeid Ra'ad Al Hussein da firaministan kasar Nawaz Sharif sun yi Allah wadai da wannan hari, kuma sun bada umurnin bada jinya ga mutanen da suka ji rauni. (Zainab)