A shekarar 2010 ne ofishin ya fitar da irin wannan takardar bayani a karo na farko. Takardar bayanin na wannan karo ya nuna yadda kasar Sin da kasashen Afrika suka inganta hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya, tare kuma da neman hanyar samun bunkasuwa tare, ciki har da inganta samun dauwamammen ci gaban cinikayya, karfafa harkokin zuba jari da tattara kudi, karfafa hadin gwiwa kan aikin gona da samar da isassun hatsi, bada tallafi ga kasashen Afrika don samar da muhimman kayayyakin more rayuwa, mayar da hankali kan neman ci gaban kasashen Afrika ta fuskokin zaman rayuwar jama'a da kara karfinsu, da kuma inganta hadin gwiwa tsakanin bangarori da dama. (Bilkisu)