Huang Chengwei ya ce, hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afrika ba ma kawai yana da muhimmanci ga sha'anin rage talauci a duniya ba, har ma zai taimaka wajen samar da jituwa a kasar Sin da Afrika. Sin na fatan nuna wa kasashen Afirka irin basira da ilmin da ta samu cikin shekaru 30 da suka gabata, ta yadda kasashen Afrika cimma nasarar rage talauci bisa yanayin da suke ciki.
Wakilin hukumar shirin raya kasashe na MDD wato UNDP dake kasar Sin Patrick Haverman ya ce, UNDP yana ta hadin gwiwa da kasar Sin a fannin sa kaimi ga hadin kai tsakanin kasashe masu tasowa. Ya yi alkawarin ci gaba da nuna goyon baya ga hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika, tare kuma da ba da gundumawa wajen tabbatar da dauwamammen ci gaba a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya. (Amina)