Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hua Chunying wadda ta bayyana hakan ta ce a lokacin ziyarar firaministan kasar Sin Li Keqiang a Afrika,ya gana da shugabannin kasashen Kenya, Uganda, Tanzaniya, Ruwanda, Sudan da Burundi da sauransu kan yadda za a raya gabashin Afrika.
Ta yi bayanin cewa bayan ganawar Shugabannin sun cimma matsaya daya kan kafa wata hanyar jirgin kasa dake hada wadannan kasashen da kuma kafa yankin raya tattalin arzikin bai daya a tsakaninsu.
Game da wannan batu, Madam Hua tayi bayani ma manema labarai a safiyar talatan nan 13 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Mr Li Keqiang ya cimma nasarar ziyarar kasashen hudu na Afrika kuma a lokacin ziyarar tasa ya halarci bikin sa hannu kan yarjejeniyar shimfida hanyar jiragen kasa tsakanin Mombasa da Nairobi na kasar Kenya. (Amina)