Mataimakin ministan al'adun kasar Sin Zhao Shaohua ya bayyana cewa, hadin gwiwa da Sin da Afrika ke yi a dukkan fannoni ciki hadda fannin al'adu ya dace da halin da ake ciki, a matsayin wani sabon sha'anin raya tattalin arziki da al'ummar bangarorin biyu, ba ma kawai al'adu ya kasance muhimmin jigo a shirin hadin gwiwa tsakaninsu ba, har ma yana da alaka da habaka hadin kai a fannin tattalin arziki da ciniki, sannan zai yi amfani sosai wajen gaggauta sabuwar dangantakar hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni cikin dogon loakci tsakaninsu.
A lokacin wannan taro da za'a rufe a ran 24 ga wata, mahalartan zasu tattauna kan wasu manyan batutuwa ciki hadda halin da ake ciki na raya sha'anin al'adu, fasahohi da aka samun, burin yin hadin kai da sauransu. Ban da haka, za a kafa wani dandalin tuntubar juna tsakanin Sin da Afrika kan sha'anin al'adu. (Amina)