A gun taron manema labaru da aka yi a laraban nan 8 ga wata a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, Madam Hua ta yi bayani dangane da tambayar da aka yi mata cewa ko ziyarar da ministan harkokin waje na kasar Sin Wang Yi ya yi a wasu kasashen Afirka a wannan karo, mataki ne da Sin ta dauka domin takara da Japan, inda Madam Hua ta ce, ziyarar ministan a nahiyar Afrika a farkon ko wace shekara, shiri ne da shugabannin kasar Sin suka dade suna yi, abin da ke nuna cewa, Sin ta dora muhimmanci sosai kan zumunci dake tsakanin bangarorin biyu. Tana mai cewa, manufar Sin a bayyane take, kuma tana kokarin sa kaimi ga kasashen duniya da su yi hadin kai da nahiyar Afrika, domin taimaka wa wajen wanzar da zaman lafiya, tabbatar da tsaro da raya Afrika. Bugu da kari, Sin na fatan kasa da kasa su daidaita tunaninsu kan aikin hadin kai da za su yi tsakaninsu da kasashen Afrika, saboda a cewar ta ya kamata su mai da hankali kan kawo amfani ga jama'ar kasashen Afrika, kada su samu kuskure a ciki. (Amina)