in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afrika ta kudu sun fara gudanar da bikin murnar shekarun kasashensu
2014-04-29 20:46:08 cri
Shekarar 2014 shekarar Afrika ta kudu ga kasar Sin kuma shekarar 2015 shekarar kasar Sin ga kasar Afrika ta kudu. Ranar 27 ga wata, rana ce ta samun 'yancin kai na kasar Afrika ta kudu, Shugaban Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar ta Afrika ta kudu Jacob Zuma sun aikawa juna wasiku domin murnar shekarun kasashensu.

A cikin wasikar da ya aika Mr Xi Jinping ya nuna cewa, kasashen biyu za su gudanar da bikin murnar kasashensu a shekarar 2014 da 2015. Inda za a shirya kasaitattun bukukuwa a fannin al'adu, wanda ya kasance muhimmin abu ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, matakin da babu shakka zai habaka fahimta da zumunci tsakaninsu da zurfafa dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, a cikin wasikarsa Mr Jacob Zuma ya ce, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta samu ci gaba sosai a shekarun nan, ya kamata, a daga matsayin mu'ammala tsakanin jama'ar kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi nan gaba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China