in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan tallafin kudin da Sin ta baiwa kasashen Afrika ya kai dala biliyan 75
2013-05-09 14:40:38 cri

Wata hukumar nazari ta kasar Amurka ta fitar da wani rahoto cewa, daga shekarar 2000 zuwa ta 2011, yawan tallafin da Sin ta baiwa kasashen Afrika 51 ya kai kimanin dala biliyan 75 wanda ya shafi ayyuka 1673.

Rahoton ya bayyana cewa, wadannan ayyuka ya shafi fannoni fiye 20 musamman ma fannin kiwon lafiya, yafe musu basusuka aikin ba da ilmi da sauransu.

Basusuka da Sin ta yafe musu ya kasance mafi yawa daga yawancin tallafin da Sin ta bayar, wanda ya zarce dala biliyan 4, sai kuma zirga-zirga da sha'anin gona da bishiyoyi da kamun kifi, sha'anin makamashi da sauransu, duk sun kasance fannonin da Sin ke yawan ba da taimakonta a kai.

Rahoton ya ce, bayan shekaru goma da suka gabata, taimako da Sin ta bayar ya shafi kusan dukkan fadin nahiyar Afrika, kuma zai kara habaka nan gaba har zai kai matsayin da Amurka ta kai a wannan fannin. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China