Saboda ganin wannan shekarar da muke ciki, shekarar Afrika ta kudu ne ga kasar Sin, hukumomin daban-daban na Afirka ta kudu sun gudanar da ayyuka masu yawa domin gabatar da alamar Afrika ta kudu a nan kasar Sin karkashin jagorancin ofishin jakadancin Afrika ta kudu. Greg Munyai ya ce, za a gudanar da shekarar Sin a Afrika ta kudu a shekara mai zuwa, gwamnatin kasar Afrika ta kudu na fatan karban karin Sinawa da su kai ziyara a Afrika ta kudu.
An kafa hukumar gabatar da alamar Afrika ta kudu a shekarar 2002 da zummar yada da kuma kafa alamar Afrika ta kudu mai kyau. Wannan hukuma ta kafa ofishinta a nan birnin Beijing a shekarar bara, da nufin baiwa Sinawa wani dandali mai kyau wajen fahimtar Afrika ta kudu, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su kara mu'ammala tsakanin su. (Amina)