Yayin ziyarar tasa, Mr Wang ya bayyana cewa, cibiyar wata shaida ce game da dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika. Tun shekaru 70 na karni na 20, Sin ta fara taimaka ma kasashen Afrika waje shimfida hanyar jirgin kasa tsakanin Tanzaniya da Zambiya, don haka wannan cibiya ta kasance aiki mafi girma da Sin ta taimaka wajen gina shi bayan hanyar jirgin kasar.
A cewar Mista Wang wadannan ayyuka sun bayyana karfin zumunci dake tsakanin Sin da Afrika tare da nuna cewa, Sin za ta cigaba da taimaka ma Afrika kuma wannan cibiyar ta bayyana goyon bayan da Sin take nunawa kokarin da kasashen Afrika suka yi wajen raya Afrika.
Ministan harkokin wajen na kasar Sin daga nan sai ya bayyana cewa a cikin wannan gini, shugabannin kasashen Afrika sun hadu domin tattauna makomar nahiyar Afrika, da yadda za su hada kai don samun bunkasuwa tsakanin su da dogaro da kansu. Hakan in ji shi ya sa, wannan gini zai shaida aikin da za a yi na raya Afrika bisa manufa bai daya da cimma muraddun kasashen Afrika.
Mr Wang wanda ya ci gaba da cewa an yi ginin da inganci don haka ya kamata, a kula da shi yadda ya kamata ta yadda za'a amfana da shi,ita kuma Sin a nata bangaren ta tura wasu kwararru domin su hada kai da abokansu na kasar Habasha da na cibiyar AU, wajen kula da wannan cibiyar.
Haka kuma Mr Wang ya yi fatan ganin jama'ar Afrika za su yi amfani da wannan cibiya yadda ya kamata, da kuma hadin kai da ma'aikatan kasar Sin ta yadda za su mai da wannan cibiyar tamkar abin tunawa da zumunci dake tsakanin jama'ar bangarorin biyu. (Amina)