Madam Hua ta yi bayanin cewa, bisa tsarin kwamitin sassan biyu za su yi musayar ra'ayoyi sosai kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya dake jawo hankulansu duka. Sin ta yi imanin cewa, ziyarar za ta inganta dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni. Hua ta kuma bayyana cewa, Sin da kasar Afrika ta kudu manyan kasashe ne masu tasowa, kuma muhimman kasashen da tattalin arzikinsu ke saurin bunkasa, saboda haka, Sin na fatan yin kokari tare da Afrika ta kudu, don daga matsayin dangantakarsu zuwa wani sabon matsayi. (Bilkisu)