Shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma, sun aikewa juna wasikun taya murnar gudanar da bukukuwan shekarun kasashen biyu.
A cikin wasikar sa, Mr Xi ya nuna cewa, aiwatar da wadannan bukukuwa a shekarar 2014 da 2015, za su kasance babban jigo ga huldar sada zumunta tsakanin kasashen biyu, abin da kuma zai sa kaimi ga kara fahimtar juna, da raya zumunta tsakanin jama'ar kasashen biyu, tare kuma da habaka dangantakar sada zumunci bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu.
A nasa bangare kuma Mr Zuma ya bayyana cewa, shekarar 2014 ta kasance shekarar kasar Sin a Afrika ta kudu, kuma shekaru 20 da kawar da manufar nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu. Don haka gwamnati, da jama'ar kasar na bayyana murnar ga cimma wadannan nasarori biyu tare da gwamnati da jama'ar kasar Sin.
Bugu da kari Mr. zuma ya ce gwamnatin Afrika ta Kudu da jama'ar ta, na dokin gudanar da wannan gagarumin biki na murnar shekarar Sin a Afrika ta kudu. (Amina)