Madam Zuma ta yi kira da a ba da muhimmanci kan yadda za a warware wasu matsalolin da kasashen Afrika ke fuskanta, a cewarta, ana matukar bukatar bunkasa sha'anin noma na zamani don kawar da talauci, lamarin dake bukatar horas da matasa yadda ya kamata, da hana matasa ficewa daga kasashensu dalilin rashin aiki yi. Idan mutane suka mai da hankali kawai kan batun tsaro, zai matuka wahala a iya warware matsalar bakin haure, saboda babu wani matakin da zai dakatar dasu ba.
Bisa labarin da kafar yada labaru ta kasar Faransa ta bayar, an ce, hukumar EU ta ba da shawara a watan Satumba na bana a ganin an gaggauta kafa wani asusu na Euro biliyan 1.8 don tinkarar wannan matsala. Kuma taron shugabannin kasashen Turai da na Afrika da za a yi a watan Disamba a Valetta na kasar Malta, zai mai da hankali kan wannan matsala ta hanyar yin hadin gwiwa tsakanin kasashen da abin ya shafa. (Amina)