Ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya ce kasarsa na fatan gabatar da wasu shawarwari, wadanda za su share fagen komawa teburin tattaunawa, tsakanin mahukuntan Isra'ila da na al'ummar Falasdinawa.
Fabius, wanda ke ziyarar aiki a gabas ta tsakiya ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar, yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa, tare da ministan harkokin waje na hukumar Falasdinawa ta PNA Reyad al-Malki.
Ya ce makasudin ziyararsa a wannan karo shi ne gabatar da shawarwari, tare da jin ta bakin masu ruwa da tsaki a yankin, ta yadda za a kai ga sake komawa teburin shawara, da tabbatar da tsaro, bayan dakatar da hakan tsahon shekaru biyu da suka gabata.
Fabius ya kara da cewa ya samu zantawa da shugaban kasar Masar Abdul Fattah Sisi, da sarki Abdullah na Jordan, da ma wasu wakilan kungiyar kasashen Larabawa, yana kuma sa ran ganawa da jami'an gwamnatin Isra'ila game da wannan batu.
Ministan ya kara da cewa a baya an sha dakatar da shawarwari tsakanin sassan biyu a matakin karshe, kasancewar ko wane bangare ba shi da burin sadaukarwa, don haka a wannan karo ake da bukatar sanya hannun kasashen ketare.
Daga nan sai ya yi gargadi da cewa, rashin shigar kasahen duniya cikin wannan lamari na iya haifar da mummunan sakamako, ba wai kawai ga yankin na gabas ta tsakiya ba, a'a har ma ga sauran kasashen duniya baki daya.(Saminu Alhassan)