Kaza lika, Mr.Hollande ya ce, ya kamata a dauki matakai yadda ya kamata domin kulla yarjejeniyar din, kana a kulla wata yarjejeniyar bin ka'idojin kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU.
A safiyar ranar 10 ga wata, gwamnatin kasar Greece ta gaskata cewa, gwamnatin ta riga ta gabatar da wani daftarin yarjejeniyar warware matsalar bashin kasar na tsawon lokaci shekaru 3 ga masu bin ta bashi, inda kasar ta bukaci masu bin bashi da su samar wa kasar taimakon kudaden Euro biliyan 53.5 cikin wadannan shekaru uku, kana bisa labarin da aka samu, an ce, gwamnatin kasar ta gabatar da daftarin din ga masu bin ta bashi da kuma majalisar kasar Greece a daren ranar 9 ga wata.
Bugu da kari, shuwagabannin mambobin kasashe 28 na kungiyar EU za su kira wani taron koli domin tattauna batun kasar Greece a ran 12 ga wata, kuma ranar za ta kasance lokacin karshe na kulla yarjejeniyar samar da taimako, kana mai iyuwa ne kasar Greece za ta janye daga yankin kudin Euro, idan bangarorin biyu ba za su iya sanya hannu kan yarjejeniyar ba a lokacin. (Maryam)