A wannan rana da karfe 3 da minti 25 da yamma, wadannan jami'ai daga kasa da kasa da shugaban kasar Faransa François Hollande sun yi jerin gwano tare da jama'ar kasar Faransa don nuna kiyayya ga ayyukan ta'addanci. Hakazalika kuma, an yi zanga-zanga a sauran birane da yankunan kasar a wannan rana. Bisa labarin da kafofin watsa labaru na kasar Faransa suka bayar, an ce, yawan mutanen da suka yi zanga-zanga a wannan rana ya kai fiye da miliyan daya.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa Bernard Cazeneuve ya bayyana a ranar 10 ga wata cewa, an yi zanga-zangar don nuna girmamawa ga mutanen 17 da suka mutu a kasar a sakamakon harin da 'yan ta'adda suka kai gare su a kwanakin baya. (Zainab)