in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shiru na minti daya a Faransa don girmama mutanen da suka mutu a harin da aka kai kan cibiyar mujallar Charlie Hebdo
2015-01-09 10:35:48 cri

A jiya da karfe 12 na tsakar rana ne, 'yan makarantu, da ma'aikatan hukumomi da kamfanonin kasar Faransa suka yi shiru na tsawon minti daya don girmama mutane 12 da suka mutu a sakamakon harin da aka kai kan cibiyar mujallar Charlie Hebdo.

Shugaban kasar Faransa François Hollande, ministan harkokin cikin gida na kasar Bernard Cazeneuve da magajiyar birnin Paris Saint-Lazare sun halarci bikin inda su ma suka yi shiru tare da 'yan sanda da ke ofishin 'yan sanda dake dab da fadar gwamnatin birnin Paris. Jama'a a birnin Paris sun hallara a babban filin dake gaban fadar gwamnatin birnin don nuna alhininsu ga mutanen da suka mutu a sakamakon harin.

Bernard Cazeneuve ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, 'yan sanda sun kama mutane 9 bayan harin da ya faru. Ban da wannan kuma, bisa hotunan da aka dauka, an tabbatar da Said Kouachi a matsayin daya daga cikin mutanen da suka kai harin. Cazeneuve ya ce, Kouachi bai taba aikata laifi a baya ba, amma yana da nasaba da wasu ayyuka masu tsattsauran ra'ayi da kanensa mai suna Cherif Kouachi ya gudanar, wanda ya shiga wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta kasar Faransa, da kuma kai wasu matasa kasar Iraki. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China