Shugaban kasar Faransa François Hollande, ya ce kasar sa na ci gaba da fuskantar barazana, don haka ya zama wajibi a maida hankali wajen dakile duk wani yunkuri na kaiwa kasar hari.
Jawabin na shugaba Hollande na zuwa ne jim kadan bayan da 'yan sandan kasar suka shawo kan wasu al'amura biyu masu alaka da yin garkuwa da mutane a kasar.
François Hollande wanda ya gabatar da wani gajeren jawabi a fadar sa, ya ce za a ci gaba da kaiwa kasar hare-hare. Don haka baya ga yabawa 'yan sanda game da matakan tsaro da suke dauka, ya kuma ya yi kira ga jama'ar kasar da su yi taka tsantsan, tare da hada kan juna. (Amina)