'Yan ta'adda sun kai hari kan muhimman abubuwan kasar Faransa, wato 'yancin fadin albarkacin baki, da yin zane zane. An bukaci kawar da mujallar Charlie Hebdo, don haka ya kamata ta ci gaba da fitowa, in ji Manuel Valls a lokacin da yake gabatar da sakonsa na fatan alheri a Evry, da aka watsa ta kafofin kasar.
Jerin gwanon masu kishin kasa na ranar Lahadi zai kasance wani babban taron gangami na jama'a da zai kasance cikin tarihin kasar, tare da fatan jerin gwanon za'a yi shi cikin karfi, da sanin ya kamata da kuma nuna karfin kasa, da darajar al'ummar Faransa, dake bayyana soyayyarta da babbar murya ga 'yancinta da hakuri da juna. Ku zo da dama, in ji faraministan kasar Faransa tare da yin alkawarin tabbatar da tsaro.
"Ta'addanci na son ya raba mu, ya kawo baraka tsakaninmu, yana fatan tsoratar da mu domin mu tsaya cikin gidajenmu. Amsa mai kyau, shi ne 'yan kasar Faransa tun daga ranar Laraba sun ci gaba da fitowa nuna yin allawadai a ko ina cikin biranen kasa", in ji mista Valls. (Maman Ada)