Ban da haka kuma a cewar Leonid Kuchma, tsohon shugaban kasar Ukraine, tawagar bangarori 3 masu ruwa da tsaki kan batun Ukraine da wakilan dakarun dake gabashin kasar sun yi taro don tattauna yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Minsk a ranar 31 ga watan Janairun da ya wuce. Sai dai dalilan da suka sa ba a cimma daidaito ba a taron su ne, da farko, shugabannin da ke wakiltar gabashin Ukraine Alexander Zakharchenko da Igor Plotnitsky, wadanda suka sa hannu kan yarjejeniyar Minsk, ba su halarci taron ba. Sa'an nan na biyu shi ne wakilan dakarun da suka halarci taron sun gabatar da bukatunsu da wa'adi na karshe, kuma sun ki tattauna shirin tsagaita bude wuta da janye manyan makamai. (Bello Wang)