A ranar Larabar da ta gabata ne dai maharan dauke da bindigogi suka kutsa kai farfajiyar gidan jaridar ta Charlie Hebdo dake birnin Paris, suka kuma bude wuta kan wasu ma'aikatan dake aiki, wanda hakan ya yi sanadiyar rasuwar mutane 12, tare da jikkata wasu 11.
Bayan abkuwar harin, 'yan sanda sun bayyana sunayen maharan su uku, wato Said Kouachi mai shekaru 34 a duniya, da Cherif Kouachi mai shekaru 32 a duniya, da kuma Hamyd Mourad mai shekaru 18 da haihuwa. Kuma tuni Hamyd Mourad ya riga ya mika kansa ga 'yan sanda.
Rahotanni sun tabbatar da cewa Said Kouachi, da Cherif Kouachi haihaffun birnin Paris ne, kuma 'yan asalin kasar Faransa. Kana daya daga cikinsu dan ta'adda ne da hukumar yaki da ta'addanci ta Faransa ta san shi sosai, yayin da daya daga cikin su ya taba samun horon amfani da makamai a kasar Yemen.
Kafofin yada labaran Faransa sun ce da ma gwamnatin Amurka ta jera sunayen wadannan mutane biyu cikin wadanda ka iya zama 'yan ta'adda.