Ya bayyana fatansa na ganin kasashen biyu sun shiga cikin wani sabon mataki na huldar dangantaka.
Dangantaka tsakanin Faransa da Morroco za ta kasance a sahun gaba a yayin babban taro kan yanayi (COP21) da zai gudana a cikin watan Disamban mai zuwa a birnin Paris da taron COP22 da zai gudana a birnin Marrakech a shekarar 2016, in ji shugaba Hollande, tare da bayyana cewa wannan ziyara za ta kasance wata babbar dama wajen yin kira a Tanger domin ganin mun cimma nasara a yayin babban taro kan yanayi da kuma himmatuwa wajen ganin duniyarmu ta dauki matakan da suka wajaba domin tabbatar da makomarmu mai kyau.
A cikin wata sanarwar da aka fitar a albarkacin wannan ziyara, fadar shugaban kasar Faransa ta nuna cewa kasar Morroco muhimmiyar kasa ce wajen janyo hankalin nahiyar Afrika domin shirya manyan tarukan duniya kan yanayi COP21 da COP22. (Maman Ada)