Bisa goron gyayyatar shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, shugaba Ali Bongo Ondimba zai halarci wannan babban macin da za'a shirya a ranar yau Lahadi a birnin Paris domin nuna jimami ga wadanda suka mutu a harin da aka kai a cibiyar mujallar Charlie Hebdo da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane goma sha biyu a ranar Laraba da safe, in ji sanarwar.
Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, shi ma zai halarci jerin gwanon, ya kuma gyayyaci shugaban kasashen tarayyar Turai kamar su faraministan kasar Spaniya Mariano Rajoy, shugaban kwamitin dattawan Italiya Matteo Renzi, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, faraministan Ingila David Cameron, faraministan Belgium Charles Michel, shugaban kwamitin tarayyar Turai Jean-Claude Juncker da shugaban kwamitin dattawan tarayyar Turai Donald Tusk.
A ranar 7 ga watan Janairu ne, Cherif da uwansa Said Kouachi suka kai hari a cibiyar mujallar Charlie Hebdo na kasar Faransa, tare da kashe mutane goma sha biyu da suka hada da shugabannin mujallar. Haka kuma wasu tagwayen hare-hare sun biyo bayan wannan hari na Charlie Hebdo a ranakun 8 da 9 ga watan Janairu a birnin Paris. (Maman Ada)