in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi kira ga Palesdinu da Isra'ila da su kaucewa tsananta halin da suke ciki
2015-10-05 14:16:33 cri

Babban magatakardan MDD Mista Ban Ki-Moon ta bakin kakakinsa ya ba da wata sanarwa a ran 4 ga wata, inda da kakkausar murya ya yi alla wadai da harin da aka kai a birnin Kudus a ran 3 ga wata, kuma ya yi kira ga shugabannin Isra'ila da Palesdinu da su yi hakuri da juna, kuma su kaucewa tsananta halin da ake ciki a halin yanzu.

Shugaban Palestinu Mahmoud Abbas ya kira mista Ban ta wayar tarho, inda ya nemi MDD da ta ba da tabbacin tsaro ga Palestinawa tun da wuri. A sa'i daya kuma, saboda ganin an kai jerin hare-hare kan 'yan Isra'ila a birnin Kudus, 'yan sanda Isra'ila sun sanar da wani mataki a wannan rana cewa, ban da mazauna wurin, 'yan kasuwa, dalibai, masu yawan shakatawa da 'yan Isra'la, ba wanda zai iya shiga Kudus a wadannan kwanaki biyu ba. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China