Feltman ya bayyana hakan ne a gun taron da kwamatin sulhu na MDD ya gudanar kan batun yankin gabas ta tsakiya, biyowa bayan rahotannin dake cewa Isra'ila ta amince da shirin gina sabbin matsugunai fiye da 1000 a gabashin birnin Kudus, matakin da kuma ya tada hankalin babban sakataren MDD Ban Ki-moon.
An dai yi hasashen cewa, aiwatar da wannan shiri, zai kawo illa ga yarjejeniyoyin da Palesdinu da Isra'ila suka cimma kan shimfida zaman lafiya. Kaza lika gina matsugunan ya sabawa dokokin kasa da kasa, da ma shirin da bangarorin biyu suka tsara game da hakan. (Zainab)