Netanyahu ya yi jawabi a gun bikin cika shekaru 19 da kisan tsohon firaministan kasar Yitzhak Rabin cewa, an kai hari ga birnin Kudus a tsakar ranar 5 ga wata bisa zugawar shugaba Abbas da kungiyar Hamas suka yi wa jama'arsu domin su aikata hakan.
A ranar 5 ga wata a birnin Kudus, an kara samun hare haren da Palesdinawa suka kai wa 'yan sanda da fararen hula a dab da hanyar jiragen kasa, wanda ya haddasa mutuwar dan sanda daya, yayin da mutane fiye da 10 suka ji rauni. Bayan abkuwar lamarin, kungiyar Hamas ta sanar da daukar alhakin kai harin a cikin sanarwarta. (Zainab)