Ranar Jumma'ar da ta gabata ne ofishin kakakin babban magatakardan MDD ya ce, MDDr ta karbi takardu 16 da Palesdinu ta gabatar, na neman shiga yarjejeniyoyin kasa da kasa, ciki had da na shiga kotun hukuntan manyan laifuffuka ta kasa da kasa.
Ofishin ya tabbatar da cewa, an mika wadannan takardu ta hannun wani jami'in MDD a birnin Ramallah a ranar 1 ga watan Janairun nan. Tuni kuma aka fara nazarin wadannan takardu, domin tsai da kuduri kan matakan da za a dauka a nan gaba.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai, zaunannen dan kallo na al'ummar Palesdinu a MDD Riyad Mansour, ya bayyana wa kafofin yada labaru a babban zauren MDD cewa ya mika wadancan takardu ga wani jami'in MDD, matakin da ya kasance muhimmanci ga Palasdinun.
Bisa tanajin dokokin, Palesdinu za ta nemi a gurfanar da sojojin Isra'ila dake kashe Palesdinawa a gaban kotu.
A ranar 30 ga watan Disambar bara ma kwamitin sulhun MDD, ya kada kuri'a kan wani daftarin shiri da kasar Jordan ta gabatar, wanda ya samu amincewar kasashen Larabawa, wanda ke bukatar Isra'ilan da ta kawo karshen mamayar da take yiwa yankunan Palesdinawa tun daga shekarar 1967, ta kuma koma teburin shawarwarin wanzar da zaman lafiya da Palesdinawa. Sai dai a karshen daftarin ya gamu da cikas, kasancewar kasashen Amurka, da Australia sun ki amincewa da shi, baya ga wasu kasashe 5 da suka kauracewa kada nasu kuri'un. (Tasallah)