in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Palesdinu: Abbas ya ce za a wargaza gwamnatin hadin gwiwa
2015-06-17 10:19:38 cri
Shugaban Palesdinu Mahmoud Abbas ya bayyana a jiya Talata cewa, za a wargaza gwamnatin hadakar kasar, don baiwa firaministan kasar iznin kafa sabuwar gwamnati.

Wata majiya ta tabbatar da cewa, Abbas ya bayyana a gun taron kungiyar Fatah a wannan rana cewa, ya tsai da kudurin wargaza gwamnatin hadakar cikin sa'o'i 24 masu zuwa, kuma za a baiwa firaministan kasar Rami al-Hamdallah iznin kafa sabuwar gwamnati. Abbas ya kara da cewa, ana sa ran majalisar gudanarwar Fatah za ta zartas da kudurin a karshe.

Rahotanni na cewa, Abbas bai bayyana dalilin tsai da wannan kuduri ba. Amma ya bayyana cewa, tun farko Hamas dake iko da zirin Gaza ba ta amince da gwamnatin hadakar da ta gudanar da ayyuka a zirin Gaza ba. Manazarta na ganin cewa, Abbas ya dauki matakin wargaza gwamnatin hadakar ce saboda gwamnatin ba ta samu wani ci gaba kan batun zirin Gaza ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China