Bisa hakan ne kuma majalisar dokokin kasar ta yi kira ga gwamnatin kasar Faransa, da ta amince Palesdinu a matsayin kasa mai 'yanci, tare da fatan za a warware matsalolin Palesdinu ta hanyar amince da ita.
A wannan rana, ministan harkokin wajen Palesdinu Riyad al-Malki ya bayyana cewa, kudurin na majalisar dokokin kasar Faransa zai sa kaimi, ga amincewa da Palesdinu a nahiyar Turai.
Kafofin watsa labaru na kasar Faransa sun tsamo sanarwar da ofishin jakadancin Isra'ila dake kasar Faransa ya fitar, wadda ke cewa kudurin zai jinkirta cimma yarjejeniyar shimfida zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
Ana dai kallon amincewar da Palesdinu ta samu a majalisar dokokin kasar Faransa a matsayin batu mai matukar ma'ana, koda yake hakan na bukatar amincewar shugaban kasar François Hollande, wanda zai bayyana matsayin karshe kan wannan batu. (Zainab)