Bisa sakamakon kuri'un da aka kada, daftarin ya samu kuri'un goyon baya 8, da na kin amincewa 2, da kuma na 'yan ba ruwan mu 5. Cikin kasashen da suka goyi bayan kudurin har da Faransa, da kasar Sin, da Jordan, da Rasha, da sauransu, sai dai a daya hannun Amurka, da Australia na cikin wadanda suka jefa kuri'ar kin amincewa.
Zaunannen wakili mai sa ido na Palesdinu dake MDD Adly Mansour, ya bayyana cewa, an tsara daftarin ne domin sa kaimi ga kwamitin sulhu, da ya dauki matakan da suka wajaba na kiyaye zaman lafiya, da karfafa gwiwar jama'ar Palesdinu. Kana ya zargi kwamitin sulhu da gaza daukar alhakin dake kan sa na samar da dama, ta warware matsalar dake wanzuwa tsakanin Isra'ila da Palesdinu a tsahon lokaci. (Zainab)