Shugaba Abbas ya bayyana hakan ne bayan sa hannun shiga wadannan hukumomi da kulla yarjejeniyoyi yayin da yake jagorantar wani taron shugabannin kwamitin kungiyar PLO a birnin Ramallah.
Abbas ya ce, Palasdinawa na da 'yancin shiga duk wata hukuma ko kulla wata yarjejeniya da nufin kafa kasar Palasdinu bisa tsarin kan iyaka da Isra'ila ta mamaye a shekara ta 1967 mai hedkwata a gabashin birnin Kudus kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada.
Ya kuma bayyana rashin jin dadinsa kan yadda kudurin ya gaza samun amincewar kuri'un da ake bukata a kwamitin sulhu na MDD. Sai dai ya yi fatan samun kuri'u 9 da ake bukata a nan gaba.
Ya kuma bayyana kudurinsa na gurfanar da kasar Isra'ila a gaban kotun na ICC kan yadda take kai hare-hare kan Palasdinawa tare da kwace masu filaye a kowa ce rana.
Shugana Abbas ya ce, hanya daya tilo ta kawo karshen rikicin yankin baki ita ce magance rikicin Palasdinu da Isra'ila . (Ibrahim)