Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin tana kira ga Isra'ila da Palesdinu da su cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta na dogon lokaci. Sannan bai kamata a ci gaba da jinkirtar bukatun al'ummar Palesdinu na neman kafa kasarsu ba.
Shi kuwa mataimakin firaministan kasar Syria kuma ministan harkokin wajen kasar Walid Muallem ya bayyana cewa, bai kamata a yi watsi da ikon jama'ar Palesdinu na komawa gidajensu da zabar makomar kasarsu da kansu ba.
Shugaban kasar Qatar Sheikh Tamim Bin Hamad al Thani ya yi kashedi cewa, yin amfani da karfin tuwo ba zai kawo karshen turjiyar da al'ummar Palesdinu ke nuna wa ba, sannan za a samar da tsaro ga jama'ar Isra'ila ne kawai ta hanyar lumana. (Zainab)