Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a cibiyar MDD dake birnin New York, yayin zaman kwamitin sulhu na MDD game da yankin gabas ta tsakiya, ya kara da cewa batun gina matsugunan yahudawa na daya daga cikin muhimman ayyukan dake kawo cikas ga wanzar da yanayin zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya. Kana gudanar da shawarwari ne kadai hanya daya tilo wajen wanzar da zaman lafiya tsakanin Palesdinu da Isra'ila.
Ya ce kasar Sin na goyon baya ga bukatu, da hakkin jama'ar Palesdinu, game da kafa kasarsu mai cin gashin kanta, kuma za ta ci gaba da kokari tare da sauran kasashen duniya wajen sa kaimi ga samun zaman lafiya a daukacin yankin gabas ta tsakiya. (Zainab)