A jiya Alhamis ne kwamitin sulhun MDD ya gudanar da muhawara game da batun yankin gabas ta tsakiya, a kuma wannan lokaci ne Wang Min ya bayyana cewa ana fuskantar rashin fahimtar juna tsakanin Palesdinu da Isra'ila, lamarin da ya haifar da mawuyacin hali a yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Ya ce a ganin kasar Sin, amfani da karfin tuwo ba zai warware sabanin dake tsakanin sassan ba, kuma kamata yayi a warware matsalar da ake fuskanta a teburin shawarwari. Wang ya ce Sin tana fatan gwamnatin kasar Isra'ila za ta dauki matakai na samar da damar gudanar da shawarwari, ciki har da dakatar da gina matsugunan yahudawa, da sakin Palesdinawa da ake tsare da su, da daina datsi hanyar zuwa zirin Gaza da dai sauransu.
Haka zalika kuma, ya kamata a maida hankali kan bukatun Isra'ila masu dacewa a fannin tsaronta.
Wang Min ya kara da cewa, ana bukatar da Palesdinu da Isra'ila, da sauran kasashen duniya su kara kokari tare, wajen warware matsalar bangarorin biyu. Ya ce Sin tana fatan za a kara amfani da tsarin shimfida zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, da nuna goyon baya ga rawar da kwamitin sulhu na MDD yake takawa kan wannan batu, da amsa bukatun da Palesdinu da kasashen Larabawa suka gabatar, da kuma daukar matakai a fannonin sa kaimi ga gudanar da shawarwari cikin lumana, tare da kammala batun mallakar zirin Gaza, da kuma sake gina zirin na Gaza. (Zainab)