in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira ga Palasdinu da Isra'ila da su maido da yin shawarwari cikin hanzari
2014-10-22 15:23:32 cri
A ranar 21 ga wata a cibiyar MDD dake birnin New York na kasar Amurka, zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi kira ga Palasdinu da Isra'ila da su tsaya tsayin daka kan yin shawarwari cikin lumana, da maido da yin shawarwari a tsakaninsu cikin hanzari don warware matsalar Palesdinu tun da wuri.

Kwamitin sulhu na MDD ya yi muhawara kan batun yankin gabas ta tsakiya a wannan rana, inda Liu Jieyi ya yi jawabi cewa, kasar Sin tana fatan Palasdinu da Isra'ila za su tsaya tsayin daka kan yin shawarwari cikin lumana, da yin amfani da damar tsagaita bude wuta a tsakaninsu wajen maido da yin shawarwarin cikin hanzari, don sa kaimi ga warware matsalar Palesdinu, daga karshe sai an kirkiro kasar Palasdinu mai cin gashin kanta da ke da hedkwatar a gabashin birnin Kudus bisa tsarin kan iyaka da aka shata a shekara ta 1967.

Ban da wannan kuma, Liu Jieyi ya yi kira ga Isra'ila da ta dakatar da gina matsugunan Yahudawa a yankin Palasdinu da ta mamaye, da sakin Palasdinawan da take tsare da su cikin hanzari, da soke kangiyar da aka yi wa zirin Gaza don samar da sharudan da suka wajaba na maido da shawarwari cikin lumana a tsakaninsu. Kasar Sin tana fatan kungiyoyi daban daban na Palasdinu za su kara hadin kansu da goyon bayan gwamnatin al'ummar Palasdinu. Haka zalika, a cewar Liu Jieyi, kamata ya yi a sa lura kan batutuwan da ke ci ma Isra'ila tuwo a kwarya. Hakkin more rayuwa da samar da zaman lafiya da tsaro kuwa nauyi ne da ya rataya a wuyan Palasdinu da Isra'ila gaba daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China