Wang Min ya bayyana hakan ne a jiya Talata, yayin muhawarar da kwamitin sulhun MDD ya gudanar, game da batun yankin gabas ta tsakiya. Ya ce warware matsalar Palesdinu da Isra'ila na da matukar muhimmanci, duba da halin rashin kwanciyar hankali da ake fama da shi yanzu haka a yankunan gabas ta tsakiya.
Wang Min ya ce, kamata ya yi Palesdinu da Isra'ila su tsaya tsayin daka wajen aiwatar da shawarwari cikin lumana. Duba da cewa shawarwarin ne kadai za su iya samar da hanyar warware matsalar bangarorin biyu, da ma batun kafuwar kasar Palesdinu, da kuma dauwwamar zaman tare cikin lumana tsakanin bangarorin biyu.
Ya ce kasar Sin na fatan bangarorin biyu za su cimma daidaito, da bin hanyar shimfida zaman lafiya, da komawa shawarwari cikin hanzari. Kana Sin na da burin ganin bangarorin biyu sun kai ga amincewar juna, da dakatar da gina matsugunai, da kawar da shinge da aka kafa a zirin Gaza. Hakazalika kuma, ya kamata a dora muhimmanci sosai ga abubuwan da kasar Isra'ila take baiwa kulawa. (Zainab)