in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta zartas da kuduri game da hakkin bil adam da yaki da tsattsauran ra'ayi
2015-10-05 14:13:14 cri

A ranar 2 ga wata ne aka rufe taron hukumar kare hakkin bil adam ta MDD karo na 30 da aka yi a birnin Geneva, inda aka zartas da kudurin da Amurka ta gabatar game da batun kare hakkin bil adam da yin rigakafi da yaki da tsattsauran ra'ayi, kudurin da Sin ba ta jefa kuri'a ba.

Bayan kada kuri'ar wakilin Sin a taron ya yi bayyani cewa, tsattsauran ra'ayi da kuma ta'addanci, dukkansu abokan gaban bil adam ne. Sin kasa ce dake fama da tsattsauran ra'ayi da ta'addanci, don haka tana adawa da duk wani nau'i na tsattsauran ra'ayi da ta'addanci. Sin tana kira ga kasashen duniya da su hada gwiwa don dakile wadannan laifufuka tare, duk wani mataki da za su dauka, kamata ya yi su bi ka'idojin MDD, da mutunta 'yancin ko wace kasa, da cikakken yankinta, kana a bar MDD da kwamitin sulhunta su taka rawar da ta dace yadda ya kamata.

Tawagar Sin a taron ta bayyana cewa, kudurin da kwamitin sulhun ya zartas bai samar da daidaito ba, sannan ba a dauki shawarar da Rasha ta gabatar a madadin Sin da sauran kasashe, na neman yi wa kuduri gyara ba. Saboda haka, Sin ta kaurace kada nata kuri'ar (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China