Kana, a cikin rahoton da aka fidda, an ce, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon na ganin cewa, taron koli zai bude wani sabon shafi wajen neman dauwamammen ci gaban duniya, a lokacin, za a kawar da talauci, samun bunkasuwa da nishadi, da kuma warware matsalar sauyin yanayi yadda ya kamata.
Bugu da kari, an ce, za a yi cikakken zaman taron shugabannin kasa da kasa a yayin da ake gudanar da taron kolin, da kuma yin shawarwari kan yadda za a iya kawar da talauci, baiwa mata iko, warware matsalar sauyin yanayi da dai sauran harkokin da ya shafi neman dauwamammen ci gaba. (Maryam)