Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Min, ya ce kasar Sin tana fatan za a kai ga zartas da shirin bunkasuwa bayan shekarar 2015, a yayin taron koli na bunkasuwa na MDD, domin kyautata muhallin da kasashe masu tasowa ke ciki, ta yadda za a inganta ci gaban duk duniya baki daya.
Mr. Wang Min wanda ya halarci taron tattauna kan takardar sakamakon neman bunkasuwa ta MDD a jiya Talata ya kuma gabatar da jawabi, ya kara da cewa kasar Sin na maraba da zartas da kudurin da taron wakilan MDD ya yi game da takardar sakamako na taron koli, na neman bunkasuwa na MDD, tare da gabatar da shirin bunkasuwa bayan shekarar 2015 ga taron koli na neman bunkasuwa na MDD domin zartas da shi. Shirin bunkasuwa bayan shekarar 2015 da aka tsara na da muhimmiyar ma'ana, zai kuma ba da jagoranci ga aikin bunkasuwa da hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa nan da shekaru 15 masu zuwa.
Bugu da kari, Wang Min ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da kokarin tabbatar da wannan shiri, da ingiza hadin gwiwar neman bunkasuwa a tsakanin kasa da kasa.(Lami)