Wang Yi ya nuna cewa, ta'addanci abokin gaban bil Adam ne, don haka bai kamata a yi amfani da ma'aunai biyu wajen yakar ayyukan ta'addanci ba. Ayyukan yakar ta'addanci na amfani da nuna karfin tuwo iri daban daban ya kamata ya zama abu mai muhimmanci ga kasashe da gamayyar kasa da kasa.
Daga bisani Wang Yi ya bayar da shawara cewa, kasar Sin tana fatan kasashen duniya za su hada kai bisa ka'idojin MDD wajen yakar ta'addanci daga dukkan fannoni, musamman a ayyukan ta'addanci da ake yi a shafukan intanet, da yin rigakafin yaduwar tsatsauran ra'ayin nuna karfin tuwo, da yunkurin toshen hanyar da 'yan ta'addan ke samun kudi da sauran tallafi da kara yin musayar bayanan sirri don yakar ayyukan ta'addanci, kana MDD ta kara taka rawa kamar yadda ya kamata. (Sanusi Chen)