in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kammala zazzafar mahawara a babban taron ta na bana
2015-10-04 13:48:30 cri
MDD ta kammala babban taron ta na shekarar nan karo na 70, sannan ta karkare da zazzafar mahawara a ranar Asabar din nan kan batutuwa da suka shafi sauyin yanayi da zaman lafiya da batun cigaban kasashen duniya.

An gabatar da batutuwa masu yawa a zauren taron, wanda aka shafe mako guda ana gudanarwa kuma shi ne karo na 70, sai dai a jawabin sa na rufe taron, shugaban taron na bana Lykketoft, ya ce akwai jan aiki a gaban kwamitin MDD.

Kimanin shugabannin kasashen duniya 120 suka gudanar da jawabai cikin mako guda a babban taron mai taken "daukar sabbin matakai bayan cikar MDD shekaru 70". Kuma dukkanin jawaban sun tabo batutuwa ne da suke bukatar daukar matakan gaggawa wadanda kasashen duniya ke fuskanta.

Kasar Sin ta yi alkawarin marawa shirin zaman lafiya na MDD baya, inda kasar ta ce zata samar da rundunar dindindin ta 'yan sandan wanzar da zaman lafiya da kuma rundunar shirin ko ta kwana ta wanzar da zaman lafiya mai dauke da dakaru dubu 8.

Shugabannin kasashen duniya sun tattauna batutuwa da suka shafi rikicin kasar Syria da matsaalar 'yan tada kayar baya da ta'addanci da matsalar 'yan gudun hijira da bakin haure. Kuma shugabannin sun tafka mahawara kan irin matakai da ya dace a dauka domin warware matsalolin da ke addabar kasashne duniya babam dabam.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China