in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane biliyan daya na duniya sun fito daga talauci a shekaru 20 da suka gabata
2015-09-15 14:01:23 cri
Kungiyar kula da harkokin ciniki da bunkasuwa ta MDD ta gabatar da rahoto a birnin Geneva a Litinin cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, mutane biliyan daya na duniya sun fita daga kangin talauci, kuma yawan mutanen da suke fama da talauci a duniya ya ragu da kashi 50 cikin dari.

A cikin rahoto mai taken "tun daga tsara shiri zuwa fara aiwatar da ayyuka" da aka gabatar, an yi nuni da cewa, mutane fiye da miliyan 100 na duniya sun zama masu arziki matsakaita a cikin shekaru 20 da suka gabata, wasu kasashe masu tasowa sun zama muhimman kasashen da suka sa kaimi ga samun bunkasuwa a duniya.

Bayan an kara yin kokari a wassu shekaru masu zuwa, watakila ba za a samu masu fama da kangin talauci a nan gaba ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China