in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude babban taron MDD karo na 70
2015-09-16 09:41:32 cri
Ana sa ran batun ci gaban muradun karni bayan shekarar 2015 ya zamo jigon babban taron MDD karo na 70 dake gudana a hedkwatar majalissar dake birnin NewYork.

Da yake tsokaci cikin jawabinsa na bude taron, shugaban zaman Mogens Lykketoft, ya ce akwai hasashen taron zai zamo mai matukar muhimmanci a tarihi, duba da cewa za a tabo batutuwa da dama wadanda ake fatan amincewa da su, a yayin taron majalissar wanda ke tafe tsakanin ranekun 25 zuwa 27 ga watan nan na Satumba.

Ana dai gudanar da taron MDDr ne a duk shekara. A bana Mr. Lykketoft daga kasar Denmark ne ke jagoran taron, an kuma zabe shi ya shugabanci zaman ne a taron MDDr a ranar 15 ga watan Yunin wannan shekara.

Kafin nadin nasa, ya jagoranci majalissar dokokin kasar Denmark tun daga shekarar 2011 zuwa farkon wannan shekara da muke ciki.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China