in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabanni 154 na kasashe da gwamnatoci za su halarci taron koli na babban taron MDD karo na 70
2015-09-21 14:03:38 cri
Wata sabuwar kididdigar da ofishin sakatariyar MDD ya bayar a ranar 17 ga wata, ta nuna cewa, shugabanni 154 na kasashe da gwamnatoci da kuma ministoci 30 ne za su halarci taron kolin neman dauwamammen ci gaba. Kana shugabanni 144 da ministoci 46 ne za su halarci taron muhawara yayin babban taron MDDr.

Kakakin babban sakataren MDD Stephane Dujarric ya bayyanawa taron manema labaru da aka shirya a hedkwatar majalisar dake birnin New York a wannan rana cewa, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon zai halarci taruka 230 a yayin babbar muhawarar, ciki har da gana da manema labaru, shawarwari tsakanin bangarori, baya ga jawabai da zai gabatar yayin taruka daban daban.

Dujarric ya kara bayyana cewa, ya zuwa yanzu ofishin sakatariyar MDD ya ba da iznin halartar taron ga wakilai guda 8915, kana da alamun cewa, za a kara ba da irin wannan iznin ga dubu dubatar wakilai kafin fara babbar muhawarar. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China