in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsaro na MDD ya sake maida takunkumin makamai da watanni tara kan Laberiya
2015-09-03 11:10:18 cri
Kwamitin tsaro na MDD ya amince bisa babban rinjaye a ranar Laraba da wani kudurin sake maida takunkumin makamai da watanni tara da aka kakabawa Laberiya tun a shekarar 2003.

Mambobin kwamitin sun kuma sake maida bisa tsawon watanni goma, wa'adin aikin gungun kwararrun dake kula sanya ido kan girmama takunkumin makaman a cikin wannan kasar.

Da yake nuna yabo a cikin kudurin, kan ci gaban da aka samu game da kokarin gwamnatin Laberiya na sake gina kasar, kwamitin tsaro ya amince da ya kawo karshen matakan da suka shafi takunkumin hana tafiye tafiye ga jami'an kasar da toshe kudaden kasar dake bankunan kasashen waje, a cewar sanarwar MDD.

Sai dai kwamtin tsaro na ganin cewa, duk da ci gaban da aka samu, matsalar Laberiya na kasancewa wata barazana ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa a shiyyar.

Dalilin haka ne mambobin kwamitin tsaro suka amince sake maida wannan takunkumi bisa makamai a kasar ta Laberiya bisa tsawon watanni tara tare da bukatar gungun kwararrun da aka kafa a shekarar 2009 da ya gabatar masa nan da ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2016 da wani rahoton karshe kan wasu korafe korafen take takunkumi, zuba kudade kan fataucin makamai da kuma cigaban da gwamnatin Laberiya ta samu wajen sanya ido da binciken makamai da iyakoki. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China