Mista Ban ya ce yana maraba da matakin da gwamnatin Somali ta dauka na sanya hannu kan dokar ta MDD kan 'yancin yara kanana, sannan ya kara da cewar, wannan mataki, tamkar wani bude wani sabon shafi ne da gwamntain Somali ta yi wanda zai tabbatar da 'yancin yara da kare mutuncinsu a fadin kasar.
MDD, ta amince da wannan kuduri ne tun a shekarar 1989 wato kimanin shekaru 26 da suka gabata.
Dokar 'yancin yaran, ta hada da 'yancin rayuwa da 'yancin kula da lafiyarsu da 'yancin ba su ilmi da yin wasanni da 'yancin rayuwa cikin iyali da 'yancin ba su kariya daga cin zarafi ko bautar da su da kuma ba su 'yancin fada a ji. (Ahmad Fagam)