Mr Ban ya yi wannan kiran ne yayin da ya ke jawabi a ranar hana gwajin makaman nukiliya ta duniya wato 29 ga watan Agustan kowa ce shekara
Ban Ki-moon ya ce, shekaru 70 da suka gabata ne aka fara gwajin makaman nukiliya a duniya, kuma hanyar da ta fi dacewa a tuna da wadanda aka yi musu laifi ita ce a daina irin wannan gwaji a nan gaba. Ya ce, yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya daga dukkan fannoni da aka zartas da ita a shekarar 1996 tana da muhimmiyar ma'ana wajen kawar da makaman nukiliya.
Kuma tun bayan shekaru 20 da suka wuce, har yanzu ba a iya fara yin amfani da yarjejeniyar ba sabo da wasu kasashen duniya ba su sa hannu kan ita ba.
Bugu da kari, Ban Ki-moon ya ce, ana maraba da kasashen dake da makaman nukiliya da su dakatar da gwajin nukiliya, a sa'i daya kuma, ya bukaci daukacin kasashen duniya da su sanya hannu da kuma zartas da yarjejeniyar hana gwajin makaman nukiliya daga dukkan fannoni. (Maryam)