Babban magatakardan MDD Mista Ban Ki-Moon ya ba da wani rahoto a ranar Jumma'a 11 ga wata, inda ya ba da shawarwari kan aikin yin kwaskwarima ga kungiyar musamman ta MDD a fannonin kiyaye zaman lafiya da daidaita harkokin siyasa, wadanda suka hada da dora muhimmanci kan rigakafi, da kyautata tsari da hanyoyin da za su bi na gudanar da ayyuka, baya ga kara hadin kai tare da hukumomin shiyya-shiyya.
A cikin wannan rahoto mai jigon "Makomar ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD" da Ban Ki-moon ya bayar bisa shawarwari daga babbar kungiyar kula da harkokin kiyaye zaman lafiya ta majalisar, an bayyana manyan sauye-sauye da MDD za ta gudana nan gaba. A cewar Mista Ban, na farko za a mai da hankali kan yin rigakafi da shiga tsakanin rigingimu, na biyu kuma, MDD na bukatar canza tsarinta tare da shirya ayyukan kiyaye zaman lafiya yadda za su wakana cikin sauri kuma a kan lokaci, ta yadda kasashe da al'ummun dake fama da tashin hankali za su amfana. Sai na uku wato za a kafa wani tsari na duniya da kuma sassa daban-daban don tinkarar kalubalolin da za a fuskanta ta fuskar zaman lafiya da tsaro, abin da aka sa gaba shi ne kara hadin gwiwa tsakanin MDD da AU.
Ban da haka kuma, Mista Ban ya jaddada makasudin gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya shi ne warware rikici ta hanyar shawarwari, ba da kariya ga fararen hula, da tabbatar da hakkinsu a fannonin lafiya, adalci da ci gaba.
Haka kuma ya bayyana cewa, MDD za ta dauki jerin matakai don kawar da matsalar yin wa fararen hula fyade da masu aikin kiyaye zaman lafiya su kan yi. (Amina)