Rahoron da nuna cewa akwai bambanci tsakanin kasashen duniya wajen gudanar da ayyukan samar da taimako ga kasashe masu tasowa. Haka kuma, ya nuna cewa tsakanin shekarar 2000 zuwa ta 2014, adadin taimakon da aka baiwa kasashe matalauta ya karu da kashi 66 bisa dari. Dangane da batun bashin da aka baiwa irin wadannan kasashe kuma, an ce galibin kasashe sun rage bashin nasu.
Sai dai a daya hannun babban magatakardan MDD Ban Ki-moon, ya nuna cewa ba a kai da cimma burin samar wa kasashe mafiya fama da talauci taimako, ko kawar da takunkumin cinikayya ga kasashe masu tasowa ba.
Burin da ake da shi a bana shi ne, gamayyar kasa da kasa su ci gaba da kudurorin shekarar 2000, wato batutuwan nan takwas na ci gaba, ciki hada da kawar da talauci, da bada ilimi, da samar da daidaito tsakanin maza da mata da dai sauransu. Kaza lika akwai bukatar cimma burikan da aka sanya gaba nan da karshen shekarar bana. (Maryam)