in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban magatakarda na MDD ya yi tir da hare-haren da aka yi a wani birnin da ke arewa maso gabashin Sham
2015-03-21 17:22:17 cri

A daren ranar 20 ga wata, ta bakin kakakinsa ne Ban Ki-moon, babban magatakardan MDD ya ba da wata sanarwa, inda ya yi tir da hare-haren da aka yi a birnin Hasaka da ke arewa maso gabashin kasar Sham, inda ake bikin murnar Nowruz a daidai lokacin abkuwar hare-haren, hare-haren da suka yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama yayin da jikkata wasu.

Sanarwar ta ce, an ba da kwarya-kwaryar rahoto da cewa, a ranar 20 ga wata, an tayar da bama-bamai sau biyu a birnin na Hasaka yayin da mazauna birnin 'yan kabliar Kurd suka yi murnar sabuwar shekara bisa kalandar Persian, inda mutane fiye da dari 1 suka mutu ko jikkata, ciki had da mata da kananan yara. Ban Ki-moon ya nuna jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren, tare da nuna fatansa na ganin wadanda suka ji rauni sun murmure.

Har wa yau Ban Ki-moon ya ce, ya lura da cewa, an labarta cewa, kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta IS tana da hannu cikin hare-haren, a yunkurin kawo baraka da bambanci a tsakanin al'ummomin Sham. Mista Ban ya ce, ko kusa ba za a bar kungiyar ta cimma mugun nufinta ba.

A cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya sake yin la'anci dukkan tashe-tashen hankali da aka yi wa fararen hula a Sham, ya kuma bukaci sassa daban daban masu gwagwarmaya da juna a Sham da su daina yin amfani da makamai idan sun ga dama a matsugunan fararen hula. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China